Matthew 2

Ziyarar Masana

1Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana,
A alʼadance Masu Hikima
daga gabas suka zo Urushalima
2suka tambaya, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas
Ko kuwa tauraro saʼad da ya taso
mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”

3Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai shi da dukan Urushalima suka damu. 4Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. 5Suka amsa suka ce, “A Betlehem a Yahudiya, gama ga abin da annabi ya rubuta:

6“ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda,
ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba,
gama daga cikinki mai mulki zai zo,
wanda zai zama makiyayin mutanena Israʼila.’
Mik 5.2

7Sai Hiridus ya kira Masanan a ɓoye, yǎ gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8Sai ya aike su Betlehem, ya ce, “Ku je ku bincika a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”

9Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Saʼan nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.

Tserewa zuwa Masar

13Bayan sun tafi, sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku tsere zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yǎ kashe.” 14Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, 15inda zai zauna sai mutuwar Hiridus. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi cewa, “Daga Masar na kirawo ɗana.”
Hos 11.1


16Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ʼyan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan. 17Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa:

18“An ji murya a Rama,
tana kuka da makoki mai tsanani,
Rahila ce take kuka domin ʼyaʼyanta,
an kāsa taʼazantar da ita,
don ba su.”
Irm 31.15

Komowa zuwa Nazaret

19Bayan Hiridus ya mutu, sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar, 20ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Israʼila, domin waɗanda suke nema su kashe yaron sun mutu.”

21Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Israʼila. 22Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wand ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi mafarki, sai ya janye zuwa gundumar Galili, 23ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa: “Za a ce da shi Banazare.”

Copyright information for HauSRK